Hanan El Tawil (also spelled Hannan Eltaweil da Hanan El Taweil; Larabci: حنان الطويل, Fabrairu 12, 1966 a Sinnuris, Faiyum- Disamba 1, 2004 a Alkahira) 'yar wasan kwaikwayo ce kuma mawaƙiya ta Masar wacce ta taka rawa a fina-finai, wasan kwaikwayo, da wasan barƙwanci. Ita ce 'yar wasan kwaikwayo ta farko ta transgender a Masar. Mutuwarta a shekara ta 2004 ana kyautata zaton ta kashe kanta ne saboda taɓin hankali wanda ya ta'azzara saboda yawan tsangwama. Ta kasance batun wani shiri na ƙungiyar masu fafutukar kare hakkin LGBTQ ta Masar No Hate Egypt.
Developed by StudentB